Isa ga babban shafi

Mali ta karbi manyan makaman yaki daga China

Gwamnatin kasar Mali ta sanar da karbar tarin motoci da makaman yaki daga hukumomin China domin taimaka mata samun galabar yakin da take gwabzawa da 'yan ta'adda a sassan kasar.

China ce kasa ta 3 da take taimakawa Mali da kayan yaki na zamani bayan wadanda kasashen Rasha da Turkiya suka bata.
China ce kasa ta 3 da take taimakawa Mali da kayan yaki na zamani bayan wadanda kasashen Rasha da Turkiya suka bata. AP
Talla

Ministan tsaro Sadio Camara ya sanar da karbar makaman lokacin gudanar da wani kwarya-kwaryar biki a Bamako wanda ya samu halartar shugaban mulkin soji Kanar Assimi Goita da wasu jami'an sa tare da Jakadan China a kasar.

Kasar Mali ta fada cikin gagarumin yaki da 'yan ta'adda da kuma masu neman raba kasar tunda daga shekarar 2012, yankin da yayi sanadiyar rasa dimbin rayuka da kuma rarrabuwar kawunan jama'ar ta.

Camara ya jinjinawa kasar China ta hannun jakadan ta dake Bamako dangane da wannan karimcin da ta musu wajen basu wadannan makamai wadanda samun su a irin wannan lokaci ke da matukar wahala.

Ministan yace makaman da aka basu da kuma jami'an da zasu horar da sojojin su wajen aiki da su zasu taimaka gaya wajen karfafa rundunar sojin kasar.

Wadannan makamai sun hada da motocin yaki na soji da na diban sojoji da na dibar marasa lafiya da kuma manyan makamai.

China ce kasa ta 3 da take taimakawa Mali da kayan yaki na zamani bayan wadanda kasashen Rasha da Turkiya suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.