Isa ga babban shafi

Sojojin Mali sun kai wani sabon farmaki a arewacin kasar

A yau litinin rundunar sojin Mali ta kai wani samame kan mayakan jihadi a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da rikici, inda mayakan da ke da alaka da kungiyar IS suka fadada ikonsu.

Tsohuwar shalkwatar rundunar G5 a Sevare na kasar Mali
Tsohuwar shalkwatar rundunar G5 a Sevare na kasar Mali REUTERS/Adama Diarra
Talla

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce an kama wasu “’yan ta’adda” goma sha biyu da kuma kayan aiki a farmakin da aka kai jiya lahadi a yankin Menaka.

Fadan dai ya faru ne a wani yanki na hamada inda a baya-bayan nan kungiyar IS ta yi galaba a kan wata kungiyar ta'addancin da ta addabi al-Qa'ida, wato Support Group for Islam and Muslim (GSIM).

Wasu daga cikin mayakan kungiyar GSIM na lasar Mali
Wasu daga cikin mayakan kungiyar GSIM na lasar Mali GSIM

Sojoji sun bukaci kungiyoyin dake dauke da makamai na cikin gida da su hada kai da sojojin Mali. Arewacin Mali shi ne yankin da a farko ya fuskanci  tashin hankali a shekara ta 2012 wanda ya lakume rayukan dubban mutane, tare da tilastawa dubban daruruwan mutane barin gidajensu tare da rura wutar juyin mulki guda biyu.

A ranar asabar, an kashe fararen hula 10 da sojoji uku, yayin da 'yan masu ikirarin jihadi da dama suka rasa rayyukan su.

Wani sojan kasar Mali yayin karbar horo kan kwarewar harba makamin Artillery.
Wani sojan kasar Mali yayin karbar horo kan kwarewar harba makamin Artillery. © REUTERS/ Paul Lorgerie/File Photo

A wani hari mafi girma da ake zargin mayakan jihadi da kaiwa  yankin filin jirgin sama na Sevare a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar, inda suka tayar da bama-bamai a cikin mota tare da kashe fararen hula 10  da jikkata wasu 61 na daban.

Fashe-fashen sun lalata wasu gidaje a kewayen filin jirgin, wanda ke da sansanin sojojin Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.