Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe akalla mutum 21 a Somaliya

Akalla mutane 21 da suka hada da kananan yara shida ne suka mutu a ambaliyar ruwan Somaliya a cikin makon da ya gabata, a cewar hukumar jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya.

Wani yanki da ambaliya ta afka wa a Mozambique
Wani yanki da ambaliya ta afka wa a Mozambique EMIDIO JOZINE / AFP
Talla

Kusan mutane 100,000 ne ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliyar ruwa ta afkawa, a yankin da fari ya shafa a gundumar Bardhere da ke yankin Gedo a kudancin Somaliya, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya.

Yankin da ambaliyar ta mamaye na kusa da kasar Habasha wato inda aka yi fama da mamakon ruwan lamarin da ya haifar da tumbatsar kogunan Shabelle da Juba.

Hukumar kula da bala'o'i ta Somaliya ta ce ambaliyar ruwan ta lalata cibiyoyin kiwon lafiya da dama.

Wasu iyalai 250 da abin ya shafa a gundumar Baardheere sun samu tallafin abinci da suka hada da shinkafa da fulawa da kuma mai daga hukumar badda agajin gaggawa ta kasar.

Hukumar kula da jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ambaliyar ruwa ta lalata makarantu hudu da dakunan wanka 200, lamarin da ya kawo cikas ga ayyukan koyo ga yara kimanin 3,000.

Rahoton na MDD ya ci gaba da cewa, sama da hekta 1,000 na filayen noma ne ruwa ya mamaye a yankin da abun ya fi kamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.