Isa ga babban shafi

Real Madrid ta fara tunanin ita ta mallaki gasar zakarun Turai - Klopp

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar Liverpool Jurgen Kloop yace sakamakon nasarorin da kunjgiyar Real Madrid ta samu wajen lashe tarin kofunan gasar zakarun nahiyar Turai, har ta fara tunanin cewar ita ta mallaki gasar baki daya.

Carlo Ancelotti tare da Jurgen Klopp
Carlo Ancelotti tare da Jurgen Klopp © Bolavip
Talla

Yayin da yake tsokaci kafin karawar da Liverpool za ta yi da Madrid a ranar Talata, Kloop yace duk da yake zasu kara wasan ne a daidai lokacin da suke mutunta Madrid saboda gwarazan ‘yan wasan da kungiyar ta mallaka, su ma zasu taka rawar da ta dace a matsayinsu na masu shirin lashe gasar.

Kocin yace Madrid na da gwarazan ‘yan wasa irin su Luka Modric da Toni Kroos da Karim Benzema da kuma Vinicious Jnr wadanda kowanne daga cikin su tauraro ne kuma abin kallo, saboda haka wasan na ranar Talata na da matukar wahala a gare su, amma kuma basu fidda shakkun samun nasara ba.

Kloop yace sun yi iya bakin kokarinsu bara har zuwa wasan karshe inda aka buge su, amma a karawa guda biyu da suka yi da Manchester City da kuma PSG, sai anyi shelar fidda su sai su farfado su samu nasara.

Mai horas da kungiyar ta Liverpool yace wannan na daya daga cikin kwarewarsu, musamman ganin wasu daga cikin ‘yan wasansu sun taba lashe gasar, kuma sun san muhimmancin ta.

Kloop yace yana fatan ganin magoya bayansu a Anfield sun tsaya da kafafuwansu domin goya musu baya wajen samun nasarar wannan karawar da za’ayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.