Isa ga babban shafi

Shugaba Buhari na halartar taro a Addis Ababa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai halarci babban taron Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, karo na 36.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kenan
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kenan © premium times
Talla

Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaban zai halarci tarukan manyan matakai guda uku kan zaman lafiya da tsaro, sauyin yanayi da kuma yanayin siyasa a wasu kasashen yammacin Afirka.

Taken taron kolin kungiyar ta AU shi ne, ''Bunkasa harkokin kasuwanci na bai daya a tsakanin kasashen Afirka."

Sanarwar ta kara da cewa, da farko akwai taron shugabannin kasashe kan makomar yankin Gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, wanda shugaban kasar Afirka ta Kudu zai jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.