Isa ga babban shafi

Sudan da Isra'ila sun cimma matsayar daidaita alakarsu

Sudan da Isra'ila sun sanar da amincewa da daidaita dangantakarsu a ziyarar aiki ta farko da ministan harkokin wajen Isra'ila ya kai Khartoum. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar dinkin Duniya ke kira ga mahukuntan kasar ta Sudan da su sauya fasalin ayyukan tsaron kasar da ke fama da kwan-gaba-kwan-baya tun bayan da Sojin kasar suka karbe iko a 2021. 

Ministan harkokin wajen Isra'ila Eli Cohen da Shugaban rikon kwaryar sojin Sudan Janar Abdel Fatah Alburhan a birin.Khartoum. 02/02/23.
Ministan harkokin wajen Isra'ila Eli Cohen da Shugaban rikon kwaryar sojin Sudan Janar Abdel Fatah Alburhan a birin.Khartoum. 02/02/23. via REUTERS - SUDAN SOVEREIGNTY COUNCIL PRESS
Talla

Tun a farko dai jagoran Sojin kasar ta Sudan Abdel-Fattah al-Burhan ya karbi bakuncin Ministan harkokin wajen kasar ta Isra’ila Eli Cohen ne a birnin Khartoom, kamin daga bisani a ga saukar Firaministan Isra’ilar  Netanyahu a wannan ziyarar da mahukuntan Sudan su ka bayyana ta a matsayin ta farko da aka taba ganin wani shugaba a Isra’ila ya kai a kasar. 

Haduwar shugabannin dai ta tattauna matakan inganta dangantakar Diplomasiyya tsakanin kasashen biyu da kuma fatar da ake ta samun hadin kai a fannin samar da tsaro a kasar da ke fama da matsaloli. 

Kasar Sudan dai ta sha fama da tashin hankali ne tun lokcin da babban Hafsan Soja Abdel Fattah al-Burhan ya karbe ragwamar ikon kasar ta hanyar kifar da gwamnatin Shugaba Umar al-Bashir a watan Okotoban 2023. 

A watan da ya gabata ma bangarori masu hamayya da juna a kasar ta Sudan sun hau Teburin tattaunawa akan batun zango na biyu na sake fasalin Siyasar kasar. 

 

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.