Isa ga babban shafi

AfDB zai zuba jarin dala biliyan 10 don mayar da Afrika cibiyar samarwa Duniya abinci

Bankin raya kasashen Afirka ya bayyana shirin zuba jarin Dala biliyan 10 nan da shekaru 5 masu zuwa domin bunkasa ayyukan noma da samar da abinci, ta hanyar da Afirka za ta zama sahun gaba wajen samarwa duniya abincin da ake bukata.  

Shugaban Bankin raya kasashen Afrika na AfBD Akinwumi Adesina.
Shugaban Bankin raya kasashen Afrika na AfBD Akinwumi Adesina. AFP
Talla

Shugaban Bankin AfDB Akinwumi Adeshina ya bayyana wannan kudiri a wajen taron bunkasa aikin noma da samar da abincin da ke gudana a kasar Senegal, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka da ministoci da kuma masana ayyukan noma da samar da abinci. 

Adeshina ya yi kira ga shugabannin 34 da suka halarci taron tare da ministoci 70 da ‘yan kasuwa da manoma da shugabannin kamfanoni da su shata irin tafarkin da za’a bi domin inganta noma a Afirka. 

Shugaban bankin ya  ce za’a samu nasarar wannan manufa ne kawai idan an hada kai domin tafiyar bai daya dan bude kofofin arzikin da Allah ya wadata nahiyar da su. 

Wannan taro na Dakar na zuwa ne bayan irin matsalolin da aka gani sakamakon annobar korona da sauyin yanayi tare da mamayar da Rasha ta yi  wa Ukraine, matsalolin da suka taimaka wajen haifar da karancin abinci a Afirka da kuma duniya. 

Yayin jawabinsa a wajen taron, shugaban kasar Senegal Makky Sall, wanda shi ne shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU, ya ce lokaci yayi da nahiyar Afirka za ta dinga ciyar da kanta ta wajen amfani da fasahar zamani domin tabbatar da ‘yancin yankin, maimakon dogaro da wasu nahiyoyi. 

Shugaban hukumar gudanarwar AU, Moussa Faki mahamat ya ce, samar da abincin da za’a ciyar da jama’ar Afirka shine sabon yakin ‘yancin da Afirka zata mayar da hankali akai domin tsayawa da kafafuwar ta, yayin da ya roki hukumomin duniya da suyi aiki tare da shirin bunkasa noman da aka yiwa suna ‘Agenda 2063’ da kuma shirin kasuwar bai daya na Afirka domin samun biyan bukata. 

Daga cikin dubban mahalarta wannan taro harda shugaban kasar Ireland Michael Higgins. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.