Isa ga babban shafi

Najeriya: Masu ruwa da tsaki a sufurin ruwa sun gudanar da babban taronsu a Lagos

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC) da hadin gwiwar takwararta ta Afirka (UASC) da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin sufurin ruwa da kuma tsaronta sun gudanar da taron kwanaki uku a birnin Lagos dake kudancin Najeriya.

Babban taron masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen ruwa na Najeriya da Afirka da ya gudana ranar litinin 16/01/23 a Oriental Hotel dake Lagos a Najeriya.
Babban taron masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen ruwa na Najeriya da Afirka da ya gudana ranar litinin 16/01/23 a Oriental Hotel dake Lagos a Najeriya. © Rfi hausa - Ahmed Abba
Talla

Taron wanda shine karo na 9 da aka bude ranar Litinin 16 ga watan Janairun 2023 karkashin jagorancin karamin ministan sufurin Najeriya, wanda ya wakilci shugaban kasar Muhammadu Buhari, nada taken “Yarjejeniyar Cinikayyar bai daya tsakananin kashen  Afrika don farfado da tattalin arzikin Nahiyar”.

Alhaji Lawal Sama’ila Abdullahi shugaban kwamitin zartarwar hukumar kula da sufurin jiragen ruwan Najeriya ya bayyana mana mahimmacin taron a zantawarsa da Ahmad Abba da ya halarci taron da ya gudana a Oriental Hotel dake Victoria Island na birnin Lagos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.