Isa ga babban shafi

Hare-haren da aka kaiwa sojojin Somaliya sun kashe akalla mutane 19

Mutane 19 ne aka kashe a tsakiyar Somaliya a wani harin bam da aka kai da mota sau biyu.

Wasu fararen hula kenan da ke duba gawawwakin 'yan 'uwansu da suka mutu a harin da aka kai Moghadishu babban birnin kasar Somalia
Wasu fararen hula kenan da ke duba gawawwakin 'yan 'uwansu da suka mutu a harin da aka kai Moghadishu babban birnin kasar Somalia AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Bayanai daga kasar sun tabbatar da cewa mayakan Al-Shabab sun dauki alhakin kai harin, kamar yadda wani kwamandan mayakan sa kai na yankin da ke kawance da gwamnati ya shaidawa AFP.

Mohamed Moalim Adan ya ce "Mutane 19 da suka hada da jami'an tsaro da fararen hula ne suka mutu sakamakon fashewar bama-baman.

Kakakin ‘yan sandan yankin ya ce motocin sun fashe ne a wata unguwa da ke cike da jama’a jim kadan da idar da sallar Asubah.

A cewar shaidun gani da ido, an jikkata mutane da dama a harin da aka kai a yankin Hiiraan, ciki har da sojoji da 'yan jarida da ke tare da su.

Mahas dai na cikin yankin da gwamnati ta kwace a farmakin da ta ke ci gaba da kai wa kungiyar da ke da alaka da al-Qaida wadda a yanzu ke rike da wasu sassan tsakiya da kudancin Somaliya tsawon shekaru.

A baya-bayan nan ne sojojin Somaliyan tare da mayakan sa-kai suka bude wata muhimmiyar hanyar samar da kayayyaki zuwa Mahas bayan da aka dade ana yi mata kawanya.

Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya sha alwashi a watan Yulin shekarar da ta gabata cewa gwamnatinsa za ta kaddamar da yaki kan mayaka masu tsattsauran ra'ayi.

Baya ga goyon bayan mayakan sa kai na cikin gida, hukumomi na iya dogaro da shirin ATMIS na Tarayyar Afirka da kuma hare-haren da Amurka ke kaiwa yayin da suke yakar masu tada kayar baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.