Isa ga babban shafi

Amurka ta ja kunnen shugabannin da zasu gudanar da zabe a 2023

Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci wasu daga cikin shugabannin kasashen Afirka da suke shirin gudanar da zabe a shekara mai zuwa da su tabbatar da cewar an gudanar da zabe mai ingancin da duniya zata amince da shi. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka Joe Biden a fadar White House
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka Joe Biden a fadar White House © vanguard
Talla

Biden ya bayyana hakane lokacin da ya gana da wasu shugabannin kasashe guda 6 a Washington wadanda kasashensu zasu gudanar da zaben shugaban kasa a shekarar 2023. 

Daga cikin wadannan shugabanni akwai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwarorinsa na kasashen Congo da Gabon da Liberia da Madagascar da kuma Saliyo. 

Mai baiwa shugaba Biden shawara akan harkokin tsaro Jack Sullivan yace ganawar ba wai Amurka na da fargaba bane dangane da zaben wadannan kasashe, sai dai bukatar taimaka musu wajen ganin an ci gaba ta fannin dimokiradiya. 

Sullivan yace fatarsu itace taimakawa ta hanyar da za’a samu karbaben zabe wanda duniya zata amince da shi. 

Kasar Amurka ta kuma jinjinawa shugaban kasar Congo Tshisekedi saboda amincewar da yayi a gudanar da zabe a kasarsa a shekara mai zuwa, abinda ya sa kasar ta bashi taimakon Dala miliyan 13 domin shirin zaben. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.