Isa ga babban shafi

Hare-haren 'yan ta'adda a Mali sun mayar da tarin garuruwa kufai

Al’ummar yankin arewa maso gabashin Mali sun fara arcewa daga gidajensu, sakamakon yadda suka firgita da kutsawar da mayaka masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiya IS ke yi.  

Taswirar yankunan da ta'addanci ya fi tsananta a Mali.
Taswirar yankunan da ta'addanci ya fi tsananta a Mali. © RFI
Talla

A watan Maris ne kungiyar IS a yankin Sahara suka kaddamar da yaki a yankunan Gao da Menaka, lamarin da ya haddasa kazamin rikici tsakaninsu da mayakan sa kai na yankin, da wasu kungiyoyi na daban da ke ikirarin jihadi.

Ganau da sauran majiyoyi sun tabbabar da cewa masu ikirarin jihadin na IS sun kutsa yankunan karkara masu hatsari, kuma masu rajin kare hakkin dan adam sun ce an kashe fararen hula.

Garuruwan Gao da Menaka sun dade suna fuskantar hare hare daga ‘yan ta’adda.

Wani magajin gari a yankin Menaka ya ce yanzu haka babu kowa a gundumarsa, sakamakon hare haren da ‘yan ta’adda ke kai musu ba kakkautawa.

Tun a shekarar 2012, dubban mutane sun mutu, kana daruruwan dubbai suka tsere daga gidajensu, sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda da suka bazu zuwa makawaftan Mali, wato Burkina Faso da Jamhuriyar Niger.

Wannan ne ma ya ingiza sojojin kasar har suka kifar da gwamnati a shekarar 2020, kuma suka dauko sojojin hayar Wagner don taimakawa wajen tabbatar da tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.