Isa ga babban shafi

Sojojin Kenya sun dira Congo domin yakar 'yan tawayen kasar

Sojojin Kenya sun isa birnin Goma na yankin gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo a wannan Asabar domin fara aikin wanzar da zaman lafiyar kasar.

Sojojin Kenya da suka isa Jamhuriyar Congo a wannan Asabar
Sojojin Kenya da suka isa Jamhuriyar Congo a wannan Asabar © kdfinfo
Talla

‘Yan Congo sun yi ta yin jinjinar ban-girma ga sojojin na Kenya jim kadan da saukarsu a filin jirgin saman a kasar.

Ana sa ran za su taimaka wajen kakkabe ‘yan tawayen M23 da suka zafafa kaddamar da hare-hare a yankin Arewacin Kivu da ke  Jamhuriyar Demokuradiyar Congo, inda har suka karbe yankuna da dama.

Sai da aka samu amincewar majalisar dokokin Kenya kafin sojojin  kasar su yi wannan balaguro zuwa Congo kuma adadinsu ya kai 900.

Tashin hankalin da ake fama da shi a Arewacin Kivu ya yi sanadiyar raba mutane sama da dubu 180 da muhallansu a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.