Isa ga babban shafi

Kenya za ta tura dakaru kusan dubu 1 Jamhuriyar Congo don yaki da 'yan bindiga

Majalisar dokokin Kenya ta amince da matakin shugaban kasar William Ruto na tura dakaru kusan dubu daya zuwa yankin Gabashin Congo mai fama da ‘yan bindiga, aikin da gwamnatin Kenya ta ce za ta kashe dala milyan 37 domin aiwatar da shi.

Wasu dakarun Kenya.
Wasu dakarun Kenya. © Thomas Mukoya/Reuters
Talla

Wadannan kudade milyan 37 za a kashe su ne a cikin watanni shidan farko don daukar dawainiyar wadannan sojoji da shugaba Ruta ya ce zai turo zuwa jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo nan ba da jimawa ba.

Wadannan dakaru dai za su aiki ne a karkashin wata runduna ta musamman da kasashen gabashin Afirka suka kafa a yunkurin murkushe kungiyoyin tawaye da ke kashe fararen hula a kasar ta Congo.

To sai dai ‘yan adawa a zauren majalisar dokokin sun nuna rashin amincewarsu a game da wannan shiri da ke bukatar makudan kudade, a daidai lokacin da al’ummar Kenya ke fama da nata matsaloli a bangaren tsaro, sannan ga dimbin bashi da ake bin kasar.

Za a dai jibge sojojin na Kenya ne a garin Goma wanda ke kusa da iyaka da Rwanda, yayin da sauran kasashen yankin da suka hada da Uganda, Burundi da kuma Sudan ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.