Kenya ta aika da sojoji zuwa Congo domin yakar 'yan tawaye - Ruto
Shugaban kasar Kenya William Ruto ya sanar da cewa, kasarsa na shirin tura dakaru zuwa gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, a wani shirin hadin gwiwa na yaki da 'yan tawaye.
Wallafawa ranar:
Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango mai arzikin ma'adinai na fafutukar ganin ta shawo kan kungiyoyin da ke dauke da makamai da dama wadanda ci gaban da suka samu a gabashin kasar a baya-bayan nan ya sake farfado da tsohuwar gaba tare da haifar da tashin hankali da makwabciyarta Ruwanda.
Shugabannin kungiyar kasashen gabashin Afirka bakwai da Kenya ke jagoranta, sun amince a watan Afrilu na kafa rundunar hadin gwiwa da za ta taimaka wajen dawo da tsaro a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
Da yake magana a wajen wani biki da aka yi a Nairobi na kaddamar da tura sojojin, Ruto ya ce an tura sojojin ne domin kare rayukan fararen hula.
Kenya ce za ta jagoranci rundunar, wanda kuma zai hada da sojoji daga Burundi, Sudan ta Kudu da Uganda.
Za a jibge dakaru na Rwanda a kan iyakar kasar, bayan da Kinshasa ta nuna adawa da da kasancewar gwamnatin Kigali cikin shirin na wanzar da zaman lafiya a Congo ba.
Rundunar sojin Kenya ta ce za a jibge rundunar na tsawon watanni shida, kuma za ta kafa sansanin kwamandojin ta a Goma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu