Isa ga babban shafi

An cimma yarjejeniyar tsagaita a kasar Habasha

Bangarorin da ke fada da juna a kazamin rikicin na tsawon shekaru biyu a yankin Tigray na kasar Habasha, sun amince da yin sulhu, in ji mai shiga tsakani na kungiyar Tarayyar Afirka, bayan tattaunawar da aka yi a Afirka ta Kudu.

'Yan tawayen na Tigray sun yaba da yarjejeniyar kuma sun ce za su mutuntu yarjejeniyar da aka kulla.
'Yan tawayen na Tigray sun yaba da yarjejeniyar kuma sun ce za su mutuntu yarjejeniyar da aka kulla. AP - Themba Hadebe
Talla

Bangarorin biyu da ke rikici a kasar dai sun amince da tsagaita bude wuta a hukumance da kuma shirin kwance damara na hadin gwiwa, in ji wakilin kungiyar AU na musamman, tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.

Yarjejeniyar ta zama sabon kwanciyar hankali ga al’ummar kaar Habasha, in ji shi, yayin wani taron manema labarai.

Tattaunawar ta tsawon mako guda ta zama tattaunawa ta farko a hukumance domin kawo karshen yakin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da haddasa kalubale ga ayyukan jin kai.

'Yan tawayen na Tigray sun yaba da yarjejeniyar kuma sun ce za su mutunta yarjejeniyar da aka kulla.

"A shirye muke mu aiwatar da kuma gaggauta tsagaita wuta karkashin wannan yarjejeniya," in ji shugaban tawagar ‘yan tawayen Tigray, Getachew Reda.

Rikicin ya barke ne a ranar 4 ga Nuwamba, 2020, lokacin da Addis Ababa ta aike da sojoji zuwa yankin Tigray bayan da ta zargi kungiyar TPLF, da ke mulkin yankin, da kai hari kan sansanonin sojojinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.