Isa ga babban shafi

An tsawaita tattaunawar zaman lafiyar Habasha a Afirka ta Kudu

An tsawaita tattaunawar zaman lafiya da ke gudana tsakanin gwamnatin Habasha da mayakan Tigray da ya kamata a kamalla ta a jiya Litinin sakamakon haske da ake ganin tataunawar na zuwa da shi.

Wasu sojojin kasar Habasha yayin atasaye a yankin Amhara, ranar 14 ga Satumban shekarar 2021.
Wasu sojojin kasar Habasha yayin atasaye a yankin Amhara, ranar 14 ga Satumban shekarar 2021. © Amanuel Sileshi AFP/File
Talla

Tattaunawa karkashin sanya idanun kungiyar kasashen Africa ta AU da ke gudana a Africa ta kudu na duba yiwuwar yadda za’a kawo karshen rikicin da aka kwashe tshaon shekaru biyu ana gwabzawa da juna lamarain kuma da ya yi sandin mutuwar daruruwan fararen hula.

Ebba Kalondo wadda ita ce kakakin shugaban gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat ta ce kawo yanzu ba’a tsayar da takamaiman lokacin da za’a karkare zaman tattaunawa ba.

Duk da dai masu shirya taron sun ki yiwa manema labarai karin bayanin dalilin tsawaita wa’adin zaman saboda alilai na tsaro, amma dai sun ce tabbas akwai ci gaba da kuma fahimtar juna a zaman.

Sai dai kuma wata majiya daga bangaren mayakan na Tigray da ta nemi a sakaya sunan ta tace akwai yiwuwar zama ya kai talatar makon gobe.

Duk da ikirarin fahimtar juna da ake samu a zaman tattaunawar, a chan yankin na Tidray kuwa ana ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun Habasha da ke samun goyon bayan na Eritria da kuma mayakan na Tigray, idan gwamnatin ke ci gaba da ruwan bama-bamai da sama da kuma jefa gurneti baji ba gani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.