Isa ga babban shafi

Wasu manyan kasashen da ke noman Koko sun kauracewa taron Brussels

Kasashen da ke kan gaba wajen noman koko a duniya, wato Ghana da Ivory Coast, sun kauracewa taron da aka yi a Brussels na gidauniyar Cocoa ta duniya wanda aka yi a ranakun 26 da 27 ga watan Oktoba.

Wani manomin Koko kenan
Wani manomin Koko kenan ©REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Hukumomi a kasashen biyu da ke yammacin Afirka na zargin kamfanonin cakuleti da ’yan kasuwa na duniya da dakile matakan inganta kudaden shigar manoman koko.

Korafe-korafen Ghana da Ivory Coast sun shafi Banbancin Kudaden da aka gindaya akan farashin dala 400 kan kowanne tan kuma ana cajin su fiye da farashin yake a kasuwar duniya

Shirin yadda za a inganta kudaden shiga na manoman koko an samar da shi ne a shekarar 2019, domin karfafa musu gwiwa, la’akari da cewa da dama daga cikinsu masu karamin karfi ne.

Amma masu sayar da kayayyaki sun sanya bambanci da ake ganin bashi da inganci ga kasashen biyu akan dala 260 na kowanne tan guda na Koko.

Kasashen biyu sun kai kusan kashi biyu bisa uku na noman koko a duniya, amma manoma a wadannan kasashe suna samun kasa da kashi 6% na kudaden shiga a masana'anun cakuleti da darajarsu ta kai sama da dala biliyan 100 a shekara.

Gidauniyar Cocoa ta Duniya, kungiyar da ke wakiltar kashi 80% na kasuwannin duniya, ta ce tarurrukanta na 2022 sun tattauna ne kan matakan inganta albashin manoma, yaki da bautar da kananan yara da kuma kawo karshen sare dazuka da ke da ake alakantawa da shi kansa Koko din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.