Isa ga babban shafi

Gwamnatin Burkina Faso ta karfafa bangaren yaki da ta'addanci

Firaministan Burkina Faso, Apollinaire Kyelem Tembela ya ce sabuwar gwamnati, ta ayyana babban burinta na tabbatar da tsaron kasar, bayan juyin mulkin da aka yi a kasar da ke yankin Sahel mai fama da rikicin masu tayar da kayar baya.

Kyaftin Ibrahim Traore, sabon shugaban gwamnatin sojin Burkina faso kenan.
Kyaftin Ibrahim Traore, sabon shugaban gwamnatin sojin Burkina faso kenan. AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

Firaministan ya bayyana haka ne bayan taron majalisar ministocin kasar na farko da Captain Ibrahim Traore ya jagoranta, wanda ya kwace mulki a farkon wannan wata.

Tembela ya ce babban burin gwamnatin yanzu shine inganta matakan tsaro, da kuma yadda za a inganta rayuwar al’ummar Burkina Faso, sai kuma yadda za a gyara tsare-tsaren gwamnati.

Y ace duk wani dan Burkina Faso da yake ganin kan sa a matsayin cikakken dan kasa, yana da damar da zai bayar da gudun mow aga ci gaban kasar.

Firaministan mai shekaru 64 a duniya yana jagorantar gwamnati membobi 23 da suka hada da jami'an soji uku ciki har da mata biyar da za su jagoranci kasar har zuwa lokacin da aka yi alkawarin dawo da mulkin farar hula.

Daga cikin muhimman mukamai a majalisar ministocin da aka bayyana, an nada Kanar Kassoum Coulibaly a matsayin ministan tsaro da kuma tsoffin sojoji, wani muhimmin mukami a kasar da tashe-tashen hankulan masu dauke da makamai suka daidaita.

Sauran jami’an biyun sun hada da Kanar Boukare Zoungrana mai kula da harkokin mulki na yankunan kasa da na tsaro da kuma Kanar Augustin Kabore mai kula da bangaren muhalli.

Ministoci biyar a gwamnatin da ta gabata a karkashin Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda aka hambarar a juyin mulkin na baya-bayan nan, za su ci gaba da kasancewa a kan matsayinsu.

An rantsar da Ibrahim Traore a matsayin shugaban rikon kwarya a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ya sha alwashin tabbatar da tsaro a kasar tare da goyan bayan mika mulki ga zabe a watan Yulin 2024. Yana da shekaru 34, shi ne shugaba mafi karancin shekaru a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.