Isa ga babban shafi

'Yan kasuwa sun shiga zanga-zanga a kasar Ghana saboda tsadar kaya

‘Yan kasuwa a babban birnin kasar Ghana Accra sun rufe shagunan su, bayan zanga zangar kwanaki 3 da suke gudanarwa kan matsalolin tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar sakamakon yakin Ukraine.

A halin yanzu dai Shugaban Ghana, Nana Akufo Addo ya shiga tsaka mai wiya sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar
A halin yanzu dai Shugaban Ghana, Nana Akufo Addo ya shiga tsaka mai wiya sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar © NIPAH DENNIS/AFP
Talla

Tuni aka rufe babbar kasuwar da ke birnin Accra, wanda ya hada da wuri mafi girma da ake siyar da kayan gyaran motoci, sai dai akwai kananan ‘yan kasuwa masu siyar da abincin ci, da gudanar da kasuwanci a gaban shagunan da ke rufe.

Kwesi Amoah, da ke kasuwancin sai da kayan gyaran motoci a kasuwar Abossey Okai, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, saboda rashin sanin tabbas ‘yan kasuwa suka daina bayar da farashin kaya kafin samo su, ganin yadda ake samun hauhawar farashi cikin dan kankanin lokaci.

A halin yanzu dai shugaban Ghana, Nana Akufo Addo ya shiga tsaka mai wuya sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar, abinda ya sa tuni ya shiga tattaunawa da hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF, don samun bashin dala biliyan 3 domin farfado da tattalin arzikin kasar.

A cikin watan Satumban da ya gabata, bashi ya yi wa Ghana katutu, wanda shine irinsa na farko a tarihi da ya kai kashi 37 cikin dari, inda darajar kudin kasar wato Cedi ya yi faduwa mafi muni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.