Isa ga babban shafi

Afirka ta Kudu ta sake jaddada goyon bayanta ga Yammacin Sahara

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sake jaddada goyan bayan kasar sa ga Yammacin Sahara wajen ganin ya zama kasa mai cin gashin kansa daga kasar Morocco.

Shugaban Afirka ta Kudu kenan, Cyril Ramaphosa
Shugaban Afirka ta Kudu kenan, Cyril Ramaphosa © AP/Nic Bothma
Talla

Ramaphosa ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi shugaban kungiyar Polisario dake fafutukar kafa kasar Yammacin Saharar, Brahim Ghali wanda ya ziyarce shi a Pretoria.

Shugaban kasar yace suna matukar damuwa da yadda kasashen duniya suka kauda kansu daga fafutukar samun yancin Yammacin Sahara wadda kasar Morocco ta yiwa kamun kazar kuku.

Ramaphosa yace su a Afirka ta Kudu sun fahimci muhimmancin wannan fafutuka ta samun yancin kan yankin, kuma suna bayyana goyan bayan su dari-bisa-dari wajen ganin an samu nasarar yancin yankin domin baiwa jama’ar yankin abinda suke bukata.

Shugaban ya danganta fafutukar ‘yancin Yammacin Sahara da na yaki da wariyar jinsin kasarsu ta Afirka ta Kudu tayi, inda ya bayyana su a matsayin halartattun yake yaken da suka zama wajibi.

Kungiyar Polisario na fafutukar samun ‘yanci kai tun daga shekarar 1976, abinda ya sa ta fada rikici da Morocco wadda ta mamaye ta tun bayan mulkin mallakar da Spain ta yiwa yankin tsakanin shekarar 1884 zuwa 1975.

Kungiyar Polisario tace akalla kasashe 80 sun amince da fafutukar su, amma kuma Morocco taki amincewa ta bata ‘yancin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.