Isa ga babban shafi

Mahamat Deby ya sha alkwashin gaggauta kafa gwamnatin hadin kan Chadi

A ranar Litiinin aka rantsar da Mahamat Idris Deby a matsayin shugaban sabuwar gwamnatin rikon kwarya da za ta share tsawon shekaru biyu kafin shirya zabuka a kasar a Chadi.

Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasar Chadi kenan, Mahamat Idris Deby
Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasar Chadi kenan, Mahamat Idris Deby © Sallau Buhari
Talla

An dai rantsar da shugaban ne bayan da taron mahawara na kasar ya amince da tsawaita wa’adin rikon kwaryar, duk da cewa wasu daga cikin ‘yan siyasa da kuma kungiyiyoyin tawaye sun kaurace wa zaman.

Da misalin karfe 10 da kwata na safe agogon kasar ta Chadi ne shuga Mahamat Idris Deby tare da rakiyar wasu manyan alkalai biyu ya shiga zauren da aka gudanar da bikin rantsar da shi a birnin Ndjamena,  kuma shigarsa a cikin zauren ke da wuya sai daruruwan mutane daga ciki da wajen kasar suka fara ihu da tafi domin yi masa lale marhabin.

A wannan karo dai shugaban ya shiga zauren ne sanye da fararen tufafi, yayin da ake gefe daya akwai manyan baki daga kasashen waje da suka hada da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da ministoci daga kasashe irinsu Nijar, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, haka zalika akwai jakadan Faransa da na Tarayyar Turai, yayin da kungiyar Tarayyar Afirka ta kaurace wa bikin.

A lokacin da yake jawabi jim kadan bayan an rantsar da shi, shugaba Mahamat Idris Deby, ya ce babban aikin da ke gabansa shi ne gaggauta kafa gwamnatin hadin kan kasar wadda za ta yi kokarin shirya zabuka don mayar da kasar karkashin cikakken tsarin dimokuradiyya.

Shugaba Deby mai shekaru 38 a duniya, ya karbi ragamar mulkin kasar ne bayan mutuwar maihaifinsa Idris Deby Itno a ranar 21 ga watan afrilun 2021, tare da jagorantar gwamnatin mulkin sojoji mai mambobi 15.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.