Isa ga babban shafi

MDD ta yi tir da mummunan kisan da aka yiwa 'yan-cirani a Libya

Majalisar Dinkin Duniya tayi Allah wadai da irin kisan gillar da aka yiwa baki 15 a Sabratha dake kusa da gabar ruwan Libya, wanda ake zargin masu safarar mutane da aikatawa.

Daya daga cikin wuraren da ake tsare da bakin haure da 'yan gudun hijira a Libya
Daya daga cikin wuraren da ake tsare da bakin haure da 'yan gudun hijira a Libya © Sara Creta
Talla

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Agaji ta Red Cross a Libya sun bayyana cewar an tsinci gawarwakin mutanen 15 a gabar ruwa ranar juma’ar da ta gabata, kuma wasu daga cikin su sun kone a cikin kwale kwale.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Libya yace duk da yake ba’a iya tantance yadda mutanen suka mutu ba, ana kyautata zaton rikici tsakanin kungiyoyin dake safarar mutanen ya shafe su.

Majalisar ta bukaci hukumomin kasar da su gaggauta daukar matakin gudanar da bincike akan lamarin domin hukunta wadanda suke da hannu a ciki.

Kasar Libya ta zama wata babbar hanyar safarar mutane daga Afirka zuwa nahiyar Turai tun bayan kawar da gwamnatin shugaba Muammar Ghadafi a shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.