Isa ga babban shafi

Burkina Faso: Faransa ta yi tir da harin da aka kai ofishin jakadancinta bayan juyin mulki

Wasu fusatattun masu zanga-zanga a Burkina Faso sun kai hari a ofishin jakadancin Faransa da ke Ouagadougou babban birnin kasar.

Wasu matasa kenan lokacin da suke shelar kin amincewa da kasancewar hannun Faransa a Burkina Faso
Wasu matasa kenan lokacin da suke shelar kin amincewa da kasancewar hannun Faransa a Burkina Faso AP - Sophie Garcia
Talla

Sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna goyon bayansu ga sabon shugaban mulkin sojin kasar, Ibrahim Traore tare da zargin Faransa da baiwa shugaban rikon kwarya Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda aka hambarar mulkin kasar.

An ci gaba da zaman rashin tabbas a birnin Ouagadougou, bayan wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar ta ce ba ta amince da kwace mulkin da sojoji suka yi ba.

Ba a dai san inda Damiba yake ba amma hukumomin Faransa sun musanta hannu tare da yin Allah wadai da tashin hankalin.

A cikin wata sanarwa da Faransa ta fitar ta ce tsaron 'yan kasarta shi ne a gabanta a halin yanzu, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

A halin da ake ciki fusatattun masu zanga-zangar sun yi ta ihun nuna kyama ga Faransa da suka hada da: "Ba ma son Faransa kuma. Ba mu son Faransa ta kasance a Afirka."

Wasu kuma na cewa: "Muna kira ga Rasha" ma’ana muna bada shawarar tsoma bakin Rasha shi ya fi dacewa da duk wani hannu da tsoffin 'yan mulkin mallaka suka sanya a kasarmu."

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce: "Muna son hadin gwiwa da Rasha. Shi ya sa muke rike da tutoci uku. Tutocin Rasha, Mali da Burkinabe."

Damiba ya yi alkawarin magance tashe-tashen hankulan masu jihadi amma masu sukar sa na zarginsa da kasancewa mai biyayya ga Faransa da ke da karfin soja a yankin.

Mai magana da yawun Faransa, Anne-Claire Legendre, ta ce ta yi Allah wadai da cin zarafin da aka yi wa ofishin jakadancin kasar, ta kuma ce zanga-zangar "aikin masu zanga-zangar adawa ne, da kuma farfaganda na rashin gaskiya da aka yi mana."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.