Isa ga babban shafi

An gano gano gawarwaki sama da 40 da aka binne a Libya

Hukumomin kasar Libya sun sanar da gano gawarwaki 42 a wani kabarin da aka binne mutane da dama a birnin Sirte, daya daga cikin yankunan da mayan IS suka rike.

Sanarwar tace tuni aka dauki kwayoyin hallita daga cikin gawarwakin domin gudanar da bincike
Sanarwar tace tuni aka dauki kwayoyin hallita daga cikin gawarwakin domin gudanar da bincike AP - Evgeniy Maloletka
Talla

Hukumar kula da mutanen da suka bata a Libya tace ma’aikanta sun zakulo gawarwaki 42 bayan samun bayanai akan kabarin.

Sanarwar tace tuni aka dauki kwayoyin hallita daga cikin gawarwakin domin gudanar da binciken likita akai.

Mayakan IS sun karbe iko da Birnin Sirte tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016 sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar, tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Moammar Ghadafi a shekarar 2011.

Kungiyar dake yaki da azabtar da mutane a duniya tace mutane sama da 500 kungiyoyin 'yan bindiga suka kashe a Libya daga watan Oktobar bara zuwa Agustan da ta gabata.

Duk da kokarin sasanta rikicin kasar Libya, har yanzu yan bindiga na ci gaba da iko da sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.