Isa ga babban shafi

Kasar Mali ta zargi Faransa da ci mata dunduniya

Firaministan rikon kwarya na kasar Mali ya yi kakkausar suka ga Faransa a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya, yana mai cewa sun fuskanci cin dunduniya lokacin da sojojin Faransa suka fice daga kasar.

Firaministan rikon kwarya na kasar Mali Abdoulaye Idrissa Maïga kenan, yayin da yake gabatar da jawabi a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya
Firaministan rikon kwarya na kasar Mali Abdoulaye Idrissa Maïga kenan, yayin da yake gabatar da jawabi a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya REUTERS - EDUARDO MUNOZ
Talla

Abdoulaye Idrissa Maïga ya ce Mali ta ji an yi watsi da ita a yakin da take yi da ta'addanci.

Duniya za ta tuna cewa, bayan watsi da Mali da aka yi a a ranar 10 ga watan Yunin 2021 bisa shawarar da Faransa ta yanke na janye sojojin Barkhane daga kasar, sai hukumomin Faransa suka fara ci wa kasar dunduniya," in ji Maiga.

“Saboda munin ayyukan da dakarun sojan Faransa suka aikata, a cikin wasikar ta mai kwanan wata 15 ga watan Agustan 2022, Mali ta bukaci taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

"Manufar wannan taro ita ce baiwa Mali damar gabatar da shaidun da ke hannunta, wanda ke nuna cewa sojojin Faransa sun sha kai wa kasata hari, " in ji Maiga.

A shekara ta 2013 ne Faransa ta shiga tsakani ta hanyar soji, lamarin da ya jagoranci yunkurin korar masu dauke da makamai daga yankunan arewacin Mali da suka mamaye.

A cikin shekaru 9 da suka gabata, Faransa ta ci gaba da kasancewarta a kasar, a wani yunkuri na tabbatar da zaman lafiya sakamakon hare-haren da 'yan tawaye ke kaiwa.

Sai dai fira ministan ya ce a yanzu fada da mayakan na hannun 'yan kasar.

"Ina so in ce al'ummar Mali sun yanke shawarar daukar makomarsu a hannunsu, suna marawa gwamnati cikakken goyon baya wajen sake gina kasar Mali da kuma dawo da tsarin mulkin kasar cikin lumana da kwanciyar hankali a watan Maris na 2024, bayan zabe mai inganci," a cewar Maiga

Maiga ya kuma soki Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres kai tsaye. Amma ya yaba da tasirin sojojin haya na Rasha da kuma "abin koyi da hadin gwiwa mai fa'ida tsakanin Mali da Rasha."

Kasashen yammaci dai na zargin sojin haya na Wagner da suka fito daga kasar Rasha, da aikata laifukan cin zarafin bil adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.