Isa ga babban shafi

Congo Brazaville ta kulla yarjejeniyar hadin kai tsakaninta da Rasha

Kasashen Congo Brazaville da Rasha sun rattaba hannu akan wata sabuwar yarjejeniyar hadin kai, abinda ke nuna dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Congo Brazaville Sassou Nguesso.
Shugaban Congo Brazaville Sassou Nguesso. © AP - Francois Mori
Talla

Ministan harkokin kasashen ketare, Denis Christel Sassou Nguesso ya sanya hannu a madadin Congo, yayin da mataimakin ministan makamashin Rasha na farko Pavel Sorokin ya sanya hannu akan yarjejeniyar ta shekaru 5.

Congo ta ki bin kasashen duniya wajen daukar matsayi dangane da yakin da ke gudana a Ukraine, sakamakon mamayar Rasha, yayin da ta shiga cikin jerin kasashe 35 da suka ki kada kuri’a a taron Majalisar Dinkin Duniya domin yin tir da mamayar da Rashar ta yi.

A nahiyar Afrika kasashe irinsu Afrika ta kudu da Angola da Mozambique da kuma Zimbabwe na matsayin dadaddun abokan Rasha saboda rawar da kasar ta taka wajen kalubalantar kama karyar turawan yamma a kasashen lokacin yakin cacar baka, yayinda yanzu haka ake ganin rawar da ta ke takawa a kasashen Libya da Mali da kuma jamhuriyar Afrika ta tsakiya duk dai a kokarin kulla alaka mai karfi tsakaninta da kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.