Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Guinea ta karyata ikirarin ECOWAS na mika mulki

Gwamnatin sojin Guinea ta zargi kungiyar ECOWAS da shara karyar cewar ta bukaci sanya mata takunkumi idan ta wuce shekaru 2 kafin mayar da mulki ga fararen hula.

Shugaban gwamnatin sojin Guinea, Kanal Amara Camara
Shugaban gwamnatin sojin Guinea, Kanal Amara Camara © Facebook/Présidence de la République de Guinée
Talla

Kanar Amara Camara, daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin Guinea yayi wannan zargi, kwana guda bayan shugaban ECOWAS Umaro Sissoco Embalo ya sanar da kulla yarjejeniya da sojojin lokacin da ya ziyarci Conakry.

A wani sakon bidiyo da Kamfanin dillancin labaran Faransa ya gani, Kanar Camara ya bayyana cewar karya da tirsasawar dake zuwa daga ECOWAS na mayar da hannun agogo, matakan da yace zasu batawa kungiyar suna.

Yayin da shugaba Embalo ke cewa sojojin Guinea sun amince su aje mulki bayan shekaru 2, Camara yace babu gaskiya cikin lamarin.

Hafsan sojin ya kuma zargi Embalo da shirya taron shugabannin ECOWAS a Amurka, sabanin yadda aka saba gudanarwa a Yankin, da zummar sanyawa kasar takunkumi, abinda yace ba zasu amince da shi ba.

Kungiyar ECOWAS ta cire takunkumin da ta sanyawa Mali bayan kasar ta gabatar da shirin mika mulki ga fararen hula a watan Maris na shekarar 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.