Isa ga babban shafi

Cote D'Ivoire ta zargi Mali da yin garkuwa da sojojinta

Kasar Cote d’Ivoire ta zargi Mali da garkuwa da sojojin ta 46 da take tsare da su na watanni biyu, bayan da kasar ta gindaya sharuddan da take bukata a cika kafin ta sake su.

Bincike ya nuna cewa an yi garkuwa da sojojin ne kafin a tsare su a kasar ta Mali
Bincike ya nuna cewa an yi garkuwa da sojojin ne kafin a tsare su a kasar ta Mali AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Wata majiya daga fadar shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ta bayyana karara cewar tsare sojojin da akayi a Mali garkuwa da su akayi, kuma kasar zata cigaba da bin hanyoyin diflomasiya domin ganin an sake su.

A watan Yuli dakarun kasar Mali suka tsare sojojin Cote d’I voire 49 da suka shiga kasar domin aikin samar da zaman lafiya, yayin da hukumomin Mali suka ce sun isa Bamako ne ba tare da izini ba.

Kama sojojin ya haifar da tabarbarewar diflomasiya tsakanin kasashen biyu, abinda ya sa shugaban kasar Togo shiga Tsakani domin warware matsalar.

A makon jiya, Mali ta saki sojoji mata guda 3 dake cikin tawagar, yayin da sauran sojoji 46 ke ci gaba da zama a tsare.

Ita dai Mali taki amincewa da bayanin dake cewa sojojin sun shiga kasar ta domin gudanar da aikin samar da zaman lafiya, saboda zargin da tayi cewa babu wanda ya shaida mata haka a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.