Isa ga babban shafi

Yara 730 ne suka mutu saboda tsananin yunwa a Somaliya - MDD

Majalisar Dinkin Duniya  ta ce kimanin yara 730 ne suka mutu a cibiyoyin abinci mai gina jiki a fadin Somaliya tun daga watan Janairu, tana mai gargadin adadin zai iya karuwa sosai, yayin da kasar ke fuskantar tsananin yunwa.

MDD ta ce kimanin yara 730 ne suka mutu a cibiyoyin abinci na Somaliya
MDD ta ce kimanin yara 730 ne suka mutu a cibiyoyin abinci na Somaliya REUTERS/Feisal Omar
Talla

Miliyoyin mutane ne ke fuskantar barazanar yunwa a kuryar gabashin Afirka, wanda ke cikin bala'in fari mafi muni a cikin shekaru arba'in bayan da aka kasa samun damina har shekaru hudu a jere, abin da ya kai ga shafe dabbobi da amfanin gona.

Wafaa Saeed, wakiliyar Somaliya a asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce, "Tamowa ta kai wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba."

"Kimanin yara 730 ne aka ruwaito sun mutu a cibiyoyin abinci mai gina jiki a fadin kasar" tsakanin watan Janairu zuwa Yuli.

"Wannan ya kai kasa da kashi daya cikin dari na yaran da aka kwantar da su, aka kuma sallame su, amma kuma muna jin cewa adadin zai iya karuwa, saboda ba a kai rahoton mutuwar yara da dama ba," in ji Wafaa Saeed.

Ta ce kimanin yara miliyan 1.5 da ke da karancin shekaru musamman kasa da biyar suna fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki, daga cikin su, 385,000 za su bukaci kulawar cutar yunwa mai tsanani.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Somaliya na gab da fuskantar yunwa a karo na biyu cikin shekaru goma kacal, kuma lokaci ya kure don ceton rayuka a kasar da ke fama da fari.

Seed ta ce fari ya janyo mummunan karancin ruwa da tsaftar muhalli, domin da yawa daga cikin wuraren ruwan sun kafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.