Isa ga babban shafi

'Yan sanda sun bude wuta kan masu zanga-zanga a Madagascar

'Yan sanda a Madagascar sun kashe mutane 14, yayin da wasu 28 suka samu raunuka lokacin da suka bude wuta akan mutanen da suke nuna fushin su, bayan kashe wani yaro zabiya.

Mutane na dauke da wani mutum da aka harba yayin arangama da 'yan sanda.
Mutane na dauke da wani mutum da aka harba yayin arangama da 'yan sanda. AFP
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace da safiyar Litinin aka samu wannan matsala a garin Ikongo dake da nisar kilomita 90 daga birnin Antananarvo.

Wani dan majalisa, Jean-Brunelle Razafintsiandraofa, yace jami’an tsaron sun bude wuta kan mai uwa da wabi abinda ya kaiga rasa rayukan.

Babban jami’in kula da lafiya na asibitin Ikongo, Tango Oscar Toky yace mutane 9 sun mutu ne nan take bayan harbin, yayin da wasu 5 suka mutu a asibiti.

Toky yace daga cikin wadanda suka samu raunuka, 9 na cikin mummunan yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.