Isa ga babban shafi

Yadda kananan kasashe suka shafe tasirin Najeriya a kungiyar ECOWAS

Kananan kasashe sun karbe tasirin da Najeriya ke da shi  kungiyar ECOWAS, duk da cewa kasar na kashe biliyoyin Naira wajen tafiyar da kungiya

Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO a Ghana
Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO a Ghana © nigeria vice president office
Talla

Wani bincike da Dailytrust ta gudanar ya nuna yadda Najeriya ke fafutukar kwato ‘yancinta na asali a cikin kasashe 15 na kungiyar, duk da cewa tana samar da kashi 60 cikin 100 na kudaden da kungiyar ECOWAS ke bukata a duk shekara.

Baya ga wannan, Najeriya na karbar bakuncin sassa uku na kungiyar ECOWAS, da suka hada da kotuna, da hukumomi, da kuma majalisar dokoki, sai dai masu lura da al'amura na ganin kasar ta gaza wajen rage kason da ta dace na ma'aikata da zabe da kuma yanke hukunci.

Yayin da tasirin Nijeriya ya kasance a cikin al'umma, kananan kasashe masu karancin gudunmawa kamar Burkina Faso, Cote d'Ivoire, Senegal, Benin, Niger, Mali, Guinea da Togo wato wadanda suka kasance Faransansa ta musu mulkin mallaka na ci gaba da baba-kere.

Kamar yadda binciken jaridar ta Daily Trust ya nuna, Najeriya bata da manyan kujeru kamar yadda ya kamata, inda kasar ta ke da kujeru hudu kacal daga cikin mukamin Darakta 32.

'Yan majalisar dokokin Najeriya sun yi barazanar ficewa daga kungiyar ECOWAS

Saboda jin zafin halin da Najeriya ke ciki a kungiyar ECOWAS, an gabatar da wani kudiri a majalisar wakilai, a watan Yuni, inda aka yi kira da a sake duba irin gudunmawar da Najeriya ke bayarwa a ECOWAS domin bunkasa zamantakewa da tattalin arziki.

Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar wakilai Awaji-inombek Abiante ya koka kan yadda Najeriya ta zuba jarin dala biliyan 1.177 a cikin kungiyar kasashen yankin ba tare da samun fa'ida mai kyau ba.

Ya ce, "A cikin shekaru 16, Najeriya ta ba da gudummawar sama da dala biliyan 1.177 ga kungiyar ECOWAS a matsayin harajin da ta dauka, kuma wannan ita ce gudunmawa mafi girma da kowace kasa ta saka tun kafuwar kungiyar”.

Hakan ta sanya Majalisar ta umurci kwamitocinta su tantance ko gudunmawar da Najeriya ta bayar ga kungiyar ta yammacin Afirka ya dace ko a'a.

ECOWAS ta musanta batun nuna son kai ga shirin daukar ma'aikata

Sai dai mataimakin shugaban kwamitin daukar ma'aikata na ECOWAS, Edwin Snowe, yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, ya ce babu kamshin gaskiya bisa zargin da ake yiwa kungiyar game da batun daukar ma’aikata.

Ya ce babu wani kuduri da aka cimma a zauren majalisar na dakatar da daukar aiki kamar yadda ‘yan majalisar dokokin Najeriya ke yi. ‘Yan Najeriya suna da isasshen wakilci a Majalisar ECOWAS da sauran cibiyoyin al’umma.

Ko wanne irin tasiri Najeriya ke da shi a ECOWAS?

Wani tsohon jakadan Najeriya a kasar Habasha kuma wakilin Najeriya na dindindin a kungiyar tarayyar Afrika Bulus Lolo, ya ce idan aka kwatanta dimbin jarin da Najeriya ke zubawa, to kuwa babu abinda sauran kasashen ke samarwa kungiyar.

"Zan yarda cewa Najeriya ba ta amfana da kungiyar duk da kasancewa kasa mafi girma a cikin kungiyar, kuma ba kawai kasa ce mafi girma ba amma mafi yawan masu ba da gudummawa. a cewar Bulus Lolo.”

Ya ce ya zuwa yau Najeriya na biyan kusan kashi 60 cikin 100, ma’ana idan ba Najeriya, da babu kungiyar ECOWAS idan ana maganar samar da kudade.

“Kuma, idan haka ne, tambaya ce da ya kamata ‘yan Najeriya su yi, nawa kasar ta amfana da kungiyar ECOWAS? in ji Bulus Lolo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.