Isa ga babban shafi

Sama da mutum 30 sun mutu yayin wani sabon rikici da ya barke a Libya

Hukumomin lafiya a kasar Libya sun ce sabon rikicin da ya barke tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawaye ya yi sanadiyyar rayukan mutum akalla 32, yayin da 159 suka samu raunuka.

An yi arangama tsakanin mayakan sa-kai da ke gaba da juna a birnin Tripoli na kasar Libya cikin dare, lamarin da ya haifar da fargabar sake komawa yakin basasa.
An yi arangama tsakanin mayakan sa-kai da ke gaba da juna a birnin Tripoli na kasar Libya cikin dare, lamarin da ya haifar da fargabar sake komawa yakin basasa. © Reuters
Talla

 

Kungiyoyin da ke dauke da makamai sun yi musayar wuta da ta lalata asibitoci da dama tare da cinnawa gine-gine wuta da yammacin ranar Juma'a, fada mafi muni a babban birnin kasar Libya da aka fuskanta, tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a shekara ta 2020.

Fadan dai ya biyo bayan takun saka tsakanin magoya bayan Abdulhamid Dbeibah da Fathi Bashagha, wadanda ke ke gaba da juna, yayin da suke fafutukar ganin sun mallaki kasar da ke arewacin Afirka, wadda ta shafe fiye da shekaru goma ana tashe-tashen hankula tun shekara ta 2011.

Gwamnatin Dbeibah da ke da shalkwata a babban birnin kasar da Majalisar Dinkin Duniya ke goya mata baya, bayan kawo karshen yakin karshe a shekarar 2020, ta hana Bashagha kafa gwamnati, tana mai cewa kamata ya yi gwamnati mai zuwa ta kasance zababbiya.

Majalisar dokokin Libya mai mazauni a gabashin kasar ta nada Bashagha a farkon wannan shekarar, inda take samun goyon bayan babban hafsan soji Khalifa Haftar, wanda yunkurinsa na kwace babban birnin kasar da karfi a shekarar 2019 ya koma yakin basasa na tsawon shekara guda.

Bashagha wanda tsohon ministan cikin gida ne, tun da farko ya yi watsi da amfani da tashin hankali wajen karbar mulki a Tripoli amma kuma daga bisani ya sauya akala tare da cewa zai iya yin amfani da karfin tuwo wajen karbe ikon kasar.

Kasar Libya ta fada cikin rudani bayan hambarar da gwamnatin shugaba Moamer Kadhafi a shekara ta 2011 tare da kashe shi a wani boren da kasashen yamma ke marawa baya, inda dubun dubatar kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma wasu kasashen ketare suka yi yunkurin cike gurbin madafun iko.

Wasu kungiyoyi masu dauke da makamai da ake ganin ba su da hannu a rikicin na baya-bayan nan sun fara goyon bayan Dbeibah a karshen wannan makon don mayar da martani na biyu game da yunkurin Bashagha na shiga babban birnin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.