Isa ga babban shafi

Atiku Abubakar ya isa Kano domin ganawa da Shekarau

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sauka a jihar Kano, inda ake sa ran zai gana da tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, wanda ya fice daga jam'iyyar NNPP a makon da ya wuce.

Ziyarar Atiku Abubakar na zuwa ne, bayan ficewar Malam Ibrahim Shekarau daga jam'iyyar NNPP
Ziyarar Atiku Abubakar na zuwa ne, bayan ficewar Malam Ibrahim Shekarau daga jam'iyyar NNPP © Atiku Abubakar
Talla

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter.

Atiku Abubakar ya samu rakiyar mataimakinsa kuma gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa, da kuma shugaban jam'iyyar PDP na kasar Iyorchia Ayu.

Daga cikin wanda suka tarbi tsohon mataimakin shugaban kasar, akwai tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido.

Ana dai sa ran dan takarar shugaban kasar zai gana da Malam Ibrahim Shekarau, wanda rahotanni ke cewa zai koma jam'iyyar ta PDP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.