Isa ga babban shafi

Fada ya sake barkewa a Habasha bayan watanni biyar da cimma yarjejeniya

Yaki na kokarin dawowa sabo a Habasha bayan da bangarorin da ke rikici da juna suka dawo da kai farmaki a yau Laraba, watanni biyar bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin kawo karshen yakin kusan shekaru 2 da kasar ta yi fama da shi a yankin Tigray.

Wasu kauyawa yayin komawa gidajensu daga cin kasuwa a garin Yechila da ke kudu maso tsakiyar yankin Tigray mai fama da rikici. 10 ga Yuli, 2021.
Wasu kauyawa yayin komawa gidajensu daga cin kasuwa a garin Yechila da ke kudu maso tsakiyar yankin Tigray mai fama da rikici. 10 ga Yuli, 2021. © REUTERS/Giulia Paravicini
Talla

A wata sanarwa da gwamnatin kasar ta Habasha ta fitar, ta zargi ‘yan tawayen yankin na Tigray da fara kaddamar da hare-hare.

Wannan dai na zaman martani ne game da zargin da ‘yan tawayen Tigray suka yiwa dakarun gwamnati, da masu taimaka musu na kaddamar da hare-hare a yankin.

Takaddamar dai ta kunno kai ne watanni biyar bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu da ke gwabza rikici a tsakanin su, wanda ya faro a watan Nuwambar 2020.

A ranar Talata ne dai, shalkwatar tsaron Habasha ta zargi ‘yan tawayen da kokarin shafawa gwamnati kashin kaji ta haryar zagin ta da fara kai musu hare-hare.

Gwamnatin Abiy Ahmed da kuma kungiyar ‘yan tawayen ta TPLF sun yi ta cacar baki a tsakanin su a ‘yan makwannin da suka gabata, duk da cewa bangarorin biyu sun tabo batun tattaunawar sulhu don kawo karshen yakin.

Bangarorin biyu dai sun kaza cimma matsaya kan wanda ya kamata ya jagoranci duk wata tattaunawa, kuma kungiyar ta TPLF ta dage cewa sai an maido da ayyukan ci gaba a yankin mai mutane miliyan shida kafin a fara tattaunawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.