Isa ga babban shafi

Somalia: Jami'an tsaro sun ceto sama da mutum 100 daga hannun Al-Shabab

Jami'an tsaron Somaliya sun ce sun ceto mutane 106 da suka makale a cikin wani otel da mayakan Al-Shabab suka kai hari a daren Juma'a.

Maharan sun yi amfani da bama-bamai wajen shiga otal din Hayat na Mogadishu kafin daga bisani su karbe iko.
Maharan sun yi amfani da bama-bamai wajen shiga otal din Hayat na Mogadishu kafin daga bisani su karbe iko. REUTERS/Feisal Omar
Talla

 

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce mutane 21 ne suka mutu inda 117 suka jikkata a cikin sa'o'i 30. Ko da yake hukumomi sun ce an kawo karshen yakin kwato otal din.

Maharan sun yi amfani da bama-bamai wajen shiga otal din Hayat na Mogadishu kafin daga bisani su karbe iko.

Kungiyar masu kaifin kishin Islama ta al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

Shugaban rundunar ‘yan sandan kasar, Abdi Hassan Mohammed Hijra, ya shaida wa manema labarai adadin wadanda aka ceto, wadanda ya ce sun hada da mata da kananan yara, amma bai bayar da adadin wadanda suka mutu ba.

Gine-ginen Otal din dai sun rushe ne bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin ‘yan bindiga da jami’an tsaro a tsawon daren Juma’a da kuma Asabar, inda faifan bidiyo ke nuna fashe-fashe da hayaki da ke fitowa daga saman rufin ginin.

'Yan uwan wadanda ake kyautata zaton suna cikin otal din a lokacin da aka kai harin, yanzu haka suna dakon sanin halin da suke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.