Isa ga babban shafi

Gwamnatin Habasha da 'yan tawaye na nunawa juna yatsa kan shirin zaman lafiya

Gwamnatin Habasha ta zargi 'yan tawayen Tigrai da haifar da cikas ga shirin  tattaunawar zaman lafiya da nufin kawo karshen yakin da aka kwashe watanni 21 ana yi a arewacin kasar.

Bangaren gwamnati dai na fatan za a shawo kan matsalar cikin sauki
Bangaren gwamnati dai na fatan za a shawo kan matsalar cikin sauki © FMM-RFI
Talla

A ‘yan makwannin da suka gabata ne dai gwamnatin Firaiminista Abiy Ahmed da kuma kungiyar ‘yan tawayen kabilar Tigrai suka tabo batun yin shawarwarin amma har yanzu akwai wasu muhimman matsaloli, inda bangarorin biyu ke zargin juna da kai ruwa rana.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar, Billene Seyoum, ta ce gwamnati na ci gaba da yin kira da a sasanta rikicin cikin lumana duk da cewa babu wata shakuwar neman zaman lafiya da kungiyar ta ‘yan tawaye ke yi.

Bangarorin biyu dai na takun-saka kan wanda zai jagoranci duk wata tattaunawa, sannan kuma kungiyar ta Tigray ta dage cewa sai an maido da ayyukan yau da kullun a yankin mai dauke da mutane miliyan shida kafin a fara tattaunawa.

Yakin da ya barke a watan Nuwamban shekarar 2020 ya bar yankin Tigrai cikin matsalar karancin abinci da rashin samun wadatattun ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da sadarwa da kuma banki.

An kashe mutane da ba a iya tantance adadinsu ba, sannan miliyoyi na bukatar agajin jin kai a yankin Tigray da yankunan da ke makwabtaka da Afar da Amhara.

Wani kwamitin gwamnati ya yi kira da a tsagaita bude a domin ba da damar sake gudanar da ayyuka a wani bangare na shawarar samar da zaman lafiya da ya shirya mikawa kungiyar Tarayyar Afirka ta AU.

Da yake mayar da martani kan kiran tsagaita bude wuta, kakakin kungiyar ta TPLF Getachew Reda, ya zargi gwamnatin kasar da yin katsalandan, ya kuma ce dakarunta suna ta tsokanar dakarun Tigray ta bangarori daban-daban.

An dais amu sassaucin rikicin a arewacin Habasha tun bayan da aka ayyana tsagaita bude wuta a karshen watan Maris, wanda zai ba da damar sake dawo da ayarin motocin agaji na kasa da kasa da ake bukata zuwa yankin Tigray bayan hutun watanni uku.

Gwamnatin Abiy ta ce duk wata tattaunawa dole ne ta kasance karkashin jagorancin wakilin kungiyar AU mai kula da yankin Afirka Olusegun Obasanjo wanda ke jagorantar yunkurin samar da zaman lafiya na kasa da kasa, amma ‘yan tawayen na son shugaban Kenya mai barin gado Uhuru Kenyatta ya shiga tsakani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.