Isa ga babban shafi

Mayakan ISWAP sun sace manoma a jihar Bornon Najeriya

Akalla manoma shida ne ake zargin mayakan ISWAP da ke ikirarin jihadi a yammacin Afirka suka yi garkuwa da su.

Mayakan ISWAP sun kwace kayan abincin 'yan gudun hijira a Bornon Njaeriya.
Mayakan ISWAP sun kwace kayan abincin 'yan gudun hijira a Bornon Njaeriya. © The Defence Post
Talla

An yi garkuwa da mutanen ne a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya ranar Laraba.

A cewar Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, ya shaidawa jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar cewa, wadanda harin ya rutsa da su galibi ‘yan gudun hijira ne, kuma sun bace ne bayan sun je gonarsu a kauyen Bulagarji da ke da nisan kilomita daga garin Mafa.

'Yan uwan wadanda abin ya shafa da suka tabbatar da faruwar lamarin, sun ce maharan sun far wa manoman ne da sanyin safiyar ranar Laraba.

Daya daga cikin ‘yan uwan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ISWAP na neman kudin fansa ne har Nera miliyan biyar kafin su sako wadanda abin ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.