Isa ga babban shafi

Buhari ya kaddamar da shirin kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a fadar shugabancin kasar da ke Abuja. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kenan
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kenan © premium times
Talla

Ana sa ran kwamitin zai aiwatar da kudurin Gwamnatin Tarayya na kawo karshen zazzabin cizon sauro a kasar.

Da yake jawabi ga majalisar mai wakilai 16 karkashin jagorancin shugaban rukunin Dangote Aliko Dangote wanda ya amince da zama jakadan yaki da cutar zazzabin cizon sauro, shugaban ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta yi dukkan mai yuwu wa wajen yaki da zazzabin cizon sauro a fadin kasar.

Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya na 2021 ya nuna cewa Najeriya ce kadai ke da kashi 27% cikin kasashen da ke fama da cutar zazzabin cizon yayin da mace-macen mata masu juna biyu ke da kashi 32%.

Cutar zazzabin cizon sauro na iya haifar da cututtuka masu tsanani da rikitarwa ga mata masu juna biyu kuma yana haifar da yawan zubewar ciki. yayin da cutar ke kashe jarirai da yara kanana.

A cewar Buhari, baya ga inganta rayuwa da lafiya da walwalar ‘yan Najeriya, dabarun da aka yi amfani da su na da fa’idoji ga bangaren kiwon lafiyar jama’a da zamantakewar tattalin arziki ga kasar.

Ya kara da cewa, a don haka kwamitin zai tabbatar da cewa kawar da cutar zazzabin cizon sauro ya kasance muhimmin abu manufofin da aka sanya a gaba.

Bugu da kari, kwamitin yaki da cutar zazzabin cizon sauron, zai samar da wani shir na neman karin kudade don kare da dorewar ci gaban da Najeriya ta samu ya zuwa yanzu, tare da dora kasar kan hanyar kawo karshen zazzabin cizon sauro da kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.