Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Mali ta gurfanar da sojojin Cote d’Ivoire kusan 50

An gurfanar da sojojin kasar Cote d’Ivoire 49 a gaban kotun Mali, inda aka tuhume su da laifin shiga kasar ba bisa izinin hukumomin kasar ba, da kuma yunkurin kifar da gwamnati, abinda ya sa alkali ya bada umurnin tsare su a gidan yari.

Kanal Assimi Goita, jagoran mulkin Soji a Mali
Kanal Assimi Goita, jagoran mulkin Soji a Mali MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Majiyar shari’ar kasar Mali tace a ranar juma’ar da ta gabata mai gabatar da kara a Bamako ya gurfanar da wadannan sojoji da aka dade ana takun saka tsakanin kasashen biyu a gaban kotu, bayan sun kwashe sama da wata guda ana tsare da su.

Kasar Cote d’Ivoire taki amincewa da tuhumar da ake yiwa sojojin nata, inda tace sun je Mali ne domin karfafa dakarun Majalisar Dinkin Duniya dake aikin wanzar da zaman lafiya a cikin kasar a karkashin rundunar MINUSMA.

Ganin yadda matsala tsakanin kasashen biyu tayi kamari, shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya shiga tsakanin inda ya gana da shugabannin kasashen da zummar samo maslaha akan yadda za’a saki sojojin da ake tsare da su, amma abin yaci tura.

Kasar Mali na zargin Cote d’Ivoire da tunzura kungiyar ECOWAS wajen sanya mata takunkumin karya tattalin arziki mai karfi, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.