Isa ga babban shafi

Bincike: Sau 29 Buhari na bayar da umarnin magance matsalar tsaro

Duk da bai wa hukumomin tsaro umarni har sau 29 cikin shekaru uku domin kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka, ‘yan Najeriya na ci gaba da rayuwa cikin fargaba sakamakon asarar rayuka da dukiyoyi da ake samu akai-akai.

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari © lailasnews
Talla

Wasu ‘yan Najeriya da masana harkokin tsaro na zargin tabarbarewar tsaro da rashin kishin kasa daga bangaren gwamnati yayin da wasu ke cewa galibin umarnin ba daga shugaban kasa ba ne kai tsaye.

Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa, bayan duk wani mummunan hari da aka kai wa ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba ko kuma a kan wata hukuma, jami’an fadar shugaban kasa kan fitar da sanarwar yin Allah wadai da wannan aika-aika tare da umurtar hukumomin soji da sauran hukumomin tsaro da su bi bayan maharan kuma kada su bari a sake faruwar lamarin.

Sai dai kuma, a mafi yawan lokuta, masu aikata laifukan kan kara aikata ta'asa jim kadan bayan kowanne umarnin shugaban kasa.

Duk da cewa a ‘yan kwanakin da suka gabata sojoji da wasu jami’an tsaro sun samu wasu nasarori ta hanyar kawar da ‘yan ta’addar Boko Haram da ‘yan bindiga da dama, wasu masana sun ce ‘yan Najeriya na bukatar karin jajircewa daga wajensu domin kawo karshen tada kayar baya a kasar da ta shafe sama da shekaru goma ana tafkawa.

A ranar 28 ga watan Maris din shekarar 2022 ‘yan ta’adda suka kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna bayan da suka tarwatsa titin jirgin, lamarin da ya tilasta wa jirgin ya kauce hanya.

A wancan lokacin an kashe fasinjoji da yawa yayin harin inda kuma aka yi garkuwa da mutum sama da 60.

Dangane da halin da shiga ne, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta dakatar da ayyukan na wani dan lokaci, yayin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga sojoji da sauran jami'an tsaro da su ceto wadanda lamarin ya shafa.

Akwai kuma wani umarnin shugaban kasa kan hare-haren ‘yan ta’adda a jihohin Sokoto, Kaduna da Filato, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dimbin dukiyoyi.

Shugaba Buhari dai ya sha suka sosai kan yadda yake tafiyar da harkokin tsaro, musamman yadda ake kashe mutane yadda da ba a saba gani ba a jihohi da dama, inda masu suka suka ce ba bu wani tasiri da umarninsa ke haifarwa illa kara dagula lamura.

Duk da yawan umarnin da shugaban kasar ya bayar, ana kashe mutane musamman a jihohin arewa yayin da ake kai hare-hare tare da sace wasu domin neman kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.