Isa ga babban shafi

Najeriya da Nijar na kokarin bunkasa harkokin kasuwancinsu a Kano

Hukumomin Najeriya da Nijar na kokarin inganta alakar kasuwanci da nufin inganta tattalin arziki a tsakanin 'yan kasuwar kasashen biyu.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © nigeria presidency
Talla

Tawagar jami’an gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun gana da hukumar gudanarwar tashar jiragen ruwa ta tsandauri wato ‘Dala Inland Dry port’ dake jihar Kano, a wani mataki na duba yadda kasashen Najeriya da Nijar zasu ci gajiyar tashar ta fannin tatalin Arziki

Tuni dai aikin shimfida layin dogo daga Najeriya zuwa Jihar Maradi ta Jamhuriyar Nijar  ya kankama, karkashin ma’aikatar sufurin Najeriyar, wanda ta nan ne za’a rinka jigilar kayyaki zuwa kasashen biyu.

Ana sa ran aikin zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar tattalin arzikin Najeriya da Nijar cikin kan kanin lokaci, ganin sabon tsarin kasuwancin da za’a aiwatar.

Latsa alamar sauti domin sauraron rahoton Abubakar Isa Dandago daga Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.