Isa ga babban shafi

An samu karuwar shekaru 10 kan hasashen yiwuwar tsawon rai ga 'yan Afrika

Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya bayyana cewar, an samu karin tsawon rayuwa cikin koshin lafiya a tsakanin ‘yan kasashen nahiyar Afirka, da kimanin karin shekaru 10, cigaban da rahoton ya ce an samu a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2019.

Rayuwar al'ummar Afrika.
Rayuwar al'ummar Afrika. AFP - RODGER BOSCH
Talla

Sakamakon binciken ya ce karin tsawon rayuwar a nhiyar ta Afirka ya zarce wanda aka gani a sauran nahiyoyin duniya a tsawon shekaru 19 da suka gabata.

Sai dai rahoton da ke kunshe cikin sanarwar da hukumar WHO ta fitar a yau, ya yi gargadin cewa mummunan tasirin annobar Korona ka iya zama barazana ga gagarumin cigaban da aka samu a Afirka.

Mataimakiyar babbar daraktan hukumar WHO mai kula da nahiyar Afirka Dakta Lindwe Makubalo ce ta jagoranci taron manema labaran da bayan kammala shi ne aka bayyana sakamakon binciken da kwararru suka gudanar kan sha’anin lafiya da rayuwa a Afirka.

Kididdigar kwararru ta nuna cewar tsakanin a yanzu haka yawan shekarun da ake sa ran dan Afirka zai yi tare da cikakkiyar lafiya ya karu zuwa 56 a shekarar 2019, idan aka kwatanta da shekaru 46 a shekara ta 2000.

Dangane da batun tsawon rayuwa kuwa, har yanzu al’ummar nahiyar Afirka ba su kai matakin hukumar lafiya ta duniya ba na fatan ganin mutane na kaiwa akalla shekaru 64 a raye, la’akari da cewar tsawon rayuwar ‘yan Afirka ya karu ne da shekaru 5.

Rahoton na hukumar WHO ya danganta cigaban da aka samu a Afirkan da samun nasarorin da aka yi wajen inganta harkokin kula da lafiya da suka hada da, kula da mata masu ciki, yara kanana, da yaki da cutuka masu saurin yaduwa ciki har da tarin fuka, da kuma dakile kaifin bazuwar cutar HIV, da Malaria, tun daga shekarar 2015.

A takaice dai an samu cigaba wajen ayyukan kula da lafiya zuwa kashi 46 cikin 100 cikin shekara ta 2019 a tsakanin kasashen Afirka, idan aka kwatanta da kashi 24 a shekarar 2000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.