Isa ga babban shafi

Tawagar Ecowas ta tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea

Tawagar masu shiga tsakani ta yammacin Afrika, cikinsu har da Shugaban Benin Thomas Boni Yayi, ta halarci birnin Conakry domin ganawa da sojojin da suka yi juyin mulki, game da jinkirin da ake samu wajen mayar da gwamnati hannun farar hula a Guinea.

Oumar Alieu TOURAY, shugaban hukumar ya samu tarba daga  Umaro Sissoco EMBALO, shugaban majalisar wakilai. na Guinea Bissau kuma shugaban taron shugabannin kasashe da na gwamnati a halin yanzu. na ECOWAS da Minista Suzie Carla BARBOSA a wannan Talata, 19 ga Yuli, 2022.
Oumar Alieu TOURAY, shugaban hukumar ya samu tarba daga Umaro Sissoco EMBALO, shugaban majalisar wakilai. na Guinea Bissau kuma shugaban taron shugabannin kasashe da na gwamnati a halin yanzu. na ECOWAS da Minista Suzie Carla BARBOSA a wannan Talata, 19 ga Yuli, 2022. © ECOWAS / CEDEAO
Talla

A wannan taro dai mahalartan sun hada da mukaddashin Shugaban Ecowas Thomas Boni Yayi, da Shugaban Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo, da jami’in diflomasiya a Ghana Omar Alieu da ma sauran jami’an diflomasiyar da suka fito daga Kasashen waje.

Tun a ranar talata da ta gabata ne mai shiga tsakani na kungiyar ecowas a Guinea, kuma tsohon shugaban Benin, Thomas Boni Yayi ya isa Kasar dan tattaunawar da ake sa ran yayi ruwa yayi tsaki wajen mayar da gwamnati hannun farar hula.                                                                                                                                                         

Kanal Mamady Doumbouya, wanda a ranar 5 ga watan Satumban 2021ya hambarar da gwamnatin Alpha Condé da ya shafe sama da shekaru 10 a karagar mulki, ya lashi takobin hannatawa farar hula mulki cikin shekaru 3 da faruwar lamarin. To saidai a ranar 3 ga watan yulin da ya gabata kungiyar ECOWAS tayi fatalli da wa’adin, ba tare da ta kakabawa Guinean da tuni aka dakatar daga kungiyar  takunkumi ba.                                              

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.