Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe mutane dubu 14 da 500 a kasashen ECOWAS

Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ta bayyana cewa, ‘yan ta’adda sun kashe akalla mutane dubu 14 da 500 tare da tilasta wa miliyan 5 da dubu 500 tserewa daga muhallansu a cikin shekaru 4 da suka gabata.

Shugaban ECOWAS mai barin gado, Jean-Claude Kassi Brou ya bayyana haka a yayin mika ragamar mulki ga sabon magajinsa.
Shugaban ECOWAS mai barin gado, Jean-Claude Kassi Brou ya bayyana haka a yayin mika ragamar mulki ga sabon magajinsa. © AFP/Nipah Dennis
Talla

Shugaban ECOWAS mai barin gado, Jean-Claude Kassi Brou ya bayyana haka a yayin mika ragamar shugabancin kungiyar ga sabon magajinsa, Dr. Omar Alieu Touray a jiya Laraba a birnin Abuja na Najeriya.

Shugaban mai barin gado ya shawarci Touray da ya zage dantse wajen yaki da yaduwar ayyukan ta’addanci a yankin kasashen Yammacin Afrika.

A cewarsa, tabarbarewar tsaro ta yi matukar illa ga yankin Sahel, inda lamarin ya shafi kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma arewa maso gabashin Najeriya, yayin da a baya-bayan ta’addancin ya fadada har zuwa kasahen Cote d’Ivoire da Benin da Togo da ke gabar ruwa.

‘Yan ta’addan dai da ‘yan bindiga sun jefa kasashen Sahel cikin zaman makoki, ganin yadda suka yi wa kimanin mutane dubu 14 da 500 kisan gilla, tare da haifar da barazana ga zaman lafiyar al’ummomin da ke rayuwa a karkara, baya ga tilasta wa miliyoyin mutane kaurace wa gidajensu a cewar Brou.

Shugaban mai barin gado ya ce, ECOWAS ta yi bakin-kokarinta wajen ganin ta tallafa wa mutanen da  rikicin ta’addancin ya mayar da su ‘yan gudun hijirar karfi da yaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.