'Yan bindiga sun kashe mutane 19 a Afirka ta Kudu
‘Yan sandan Afirka ta Kudu sun ce hare-haren bindiga kashi biyu, a wani gari kusa da birnin Johannesburg, da kuma wani a gabashin kasar, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19.
Wallafawa ranar:
A cikin sanrwar da suka fitar a yau Lahadi, ‘yan sanda sun ce, a garin Soweto, mutane 15 aka kashe a lokacin da suke shakatawa cikin dare, lokacin da maharan da suka isa mashayar cikin karamar motar bas suka bude wuta kan mutanen dake wurin.
A gabashin birnin Pietermaritzburg kuwa, jami’an tsaro sun ce mutane hudu suka mutu, wasu takwas kuma. suka jikkata, bayanda wasu ‘yan bindiga biyu suka budewa wuta kan mutane dake shakatawa a wata mashaya.
Majiyoyin 'yan sanda sun ce ya yi wuri a alakanta hare-haren biyu, said ai babu shakkah kan kamanceceniyar da suka yi da juna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu