Cote d'Ivoire ta ware dala miliyan 405 don kange barazanar 'yan ta'adda
Gwamnatin Cote d’Ivoire ta sanar da ware dala milyan 405 domin karfafa tsaro a kan iyakar kasar da Burkina Faso da kuma Mali wadanda ke fama da ayyukan ta’addanci.
Wallafawa ranar:
Mamadou Touré, ministan samar wa matasan kasar ayyukan yi, ya ce za a yi amfani da wadannan kudade ne wajen samar wa matasa ayyukan yi, wanda zai hana su mara wa ayyukan ta’addanci baya.
Tun bayan tsanantar ayyukan ta'addanci a makwabtanta, gwamnatin Cote d'Ivoire ta daura damarar wayar da kan matasa da nufin hana su shiga makamantan ayyukan.
Haka zalika ma'aikatar tsaro ta karfafa jami'an tsaro a kan iyakokin kasashen 2 baya ga tsananta bincike kan duk da wani zargi kan daidaikun mutane ko kuma kungiyoyi duk dai a kokarin hana fantsamuwar kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu