Isa ga babban shafi

Ana gab da fasalta kundin tsarin mulkin Libya

An  shiga rana ta 4 a jere da fara taron masu ruwa da tsaki don fasalta kundin tsarin mulkin kasar Libya da Masar ke jagoranta a birnin Cairo, a wani yunkuri na ganin an gudanar da zaben kasar da ta shafe shekaru ta na fama da rikici.

'Yan kasar Libya sun kagu a gudanar da zabe
'Yan kasar Libya sun kagu a gudanar da zabe REUTERS - ESAM OMRAN AL-FETORI
Talla

Shiga tsakanin na Masar bisa jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da aka faro a Lahadin da ta gabata, shi ne karo na 3 da ake gudanarwa a kokarin tabbatar da zaman lafiya a kasar da kuma gudanar da zabe.

Ana saran a shafe fiye da mako guda ana zaman tattaunawar wanda zai bayar da damar bibiyar kundin tsarin mulkin kasar da zai bayar da damar gudanar da zabe a kasar.

Taron ya kunshi mambobin majalisar Libya, da na babban kotun kasar da kuma bangarorin masu bayar da shawarwari baya ga kwararru daga bangarorin siyasa dukkaninsu bisa sanya idanun Majalisar Dinkin Duniya.

Babbar jami’Majalisar Dinkin Duniya da ke sanya idanu kan rikicin na Libya ya roki bangarorin da ke cikin tattaunawar su samar da gamsasshiyar matsaya da za ta kawo karshen rikicin siyasar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.