Isa ga babban shafi

'Yan Birtaniyya na zanga-zangar adawa da korar masu neman mafaka zuwa Rwanda

Masu fafutukar wajen nuna adawa da manufofin gwamnatin Birtaniya na tura bakin haure zuwa Rwanda sun ce za su daukaka karar su zuwa kotun daukaka kara a litinin din nan.

Wasu 'Yan Birtaniyya sun yi zanga-zangar adawa da korar 'yan gudun hijira zuwa Rwanda.
Wasu 'Yan Birtaniyya sun yi zanga-zangar adawa da korar 'yan gudun hijira zuwa Rwanda. AP - Frank Augstein
Talla

Hakan na zuwa ne bayan da babbar kotun kasar ta ce jirgin farko dauke da masu neman mafaka kimanin 31 daga Birtaniya zai nufi kasar Rwanda ranar Talata, kafin wasu su bi sahu daga bisani.

Sai dai masu fafutukar da suka shigar da karar ta farko a babbar kotun, sun ce sun damu matuka kan halin da mutanen da aka shirya tilasta maida su gida zasu shiga don haka su ke kokarin hana tashin jirgin na farko.

Da yake magana a babban kotun a ranar Juma'a, Justice Swift ya ce bayyi la’akari da akwai wata hujja da zai sanya a ki kulada masu neman mafaka ba.

Sai dai ya ce za a sake nazarin shari’ar, inda babbar kotun za ta saurari daukaka karar manufar baki daya, kafin karshen watan Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.