Isa ga babban shafi

An tsige matar da ke shirin binciken shugaban kasa

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya dakatar da shugabar hukumar yaki da cin hanci da rashawar a kasar Busisiwe Mkhwebane bayan ta sanar da kaddamar da bincike akan zargin tarin kudaden da shugaban ya boye a gonarsa wanda barayi suka sace.

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa © Esa Alexander/Pool via REUTERS
Talla

Tsohon shugaban kasa Jacob Zuma ya nada Busisiwe lokacin da yake rike da karagar mulki, abin da ya sa ake kallon cewar an nada ta ne domin kare shi daga tuhume tuhumen da ake masa na cin hanci da rashawa.

Majalisar dokokin kasar da ke dauke da akasarin magoya bayan shugaba Ramaphosa ta kaddamar da shirin gudanar da bincike akan ta a watan jiya da zummar tube ta daga mukamin.

Sanarwar fadar shugaban kasar ta ce an dakatar da Mkhwebane har zuwa lokacin da majalisa za ta kammala bincike akan ta.

Wannan dakatarwar na zuwa ne kwana guda bayan Mkhwebane ta ce za ta gudanar da bincike akan yadda shugaban kasar yayi rufa rufa akan fashin da aka masa bara lokacin da barayi suka shiga gidan gonar sa suka kuma samu kudin da ya kai Dala miliyan 4.

Fadar shugaban kasar tace mataimakin Mkhwebane zai karbi aikin ta da kuma ci gaba da gudanar da harkokin hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.