Isa ga babban shafi

Sama da mutane 6,000 aka kashe a cikin watanni 3 a Afrika ta Kudu

Ministan ‘yan sandan Afrika ta Kudu Bheki Cele ya ce yawaitar kashe kashen da ake samu da kuma aikata ta’addanci ya sanya kasar a sahun gaba a cikin jerin kasashen da ke da hatsari a duniya.

Shugaban 'yan sandan Afrika ta Kudu Bheki Cele.
Shugaban 'yan sandan Afrika ta Kudu Bheki Cele. AFP
Talla

A lokacin wani taron manema labarai da ya gudanar a juma’ar nan, ya ce a watannin ukun farko na wannan shekarar an kashe mutane dubu 6 da 83 wanda hakan ya nuna an samu karuwar kashi 22.2 idan aka kwatanta da wanda aka samu a irin wannan lokacin a shekarar da ta gabata.

Kashe kashen ya shafi yara 306 wanda shima ya nuna an samu karuwar kashi 37.2.

Ya ce an samu karuwar aikata laifukan fyade inda aka yi wa mutane dubu 10 da dari 818 sannan kuma aka yi garkuwa da mutane dubu 3 da dari 306.

Ministan yayi alkawarin cire gurbatattun jami’an ‘yan sanda daga aiki da kuma samar da kayan aikin da jami’an ‘yan sada ke bukata don inganta aikin dan sanda a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.